Yayin da Mr. Liu ya ba da rahoton aikin tallafawa matalauta a kauyuka ga zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar, ya bayyana cewa, daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2012, yawan matalauta a kauyukan kasar Sin ya ragu daga kashi 17.2 cikin 100 zuwa kashi 10.2 cikin 100.
Amma bisa kididdigar da ofishin tallafawa matalauta ya bayar, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2012, yawan matalauta a kasar Sin ya kai kimanin miliyan 100.
Liu Yongfu ya ce, nan gaba, kasar Sin za ta yi gyare-gyare tare da kirkiro da sabbin hanyoyin tallafawa matalauta, da yin bincike game da batutuwa da suka shafi talauci a kauyuka da nazarin abubuwan da ke janyo talauci, don ba da tallafi ga matalauta daidai gwargwado, da fidda manufofin tallafa musu, da kafa dokoki don ba da tabbaci ga aikin tallafawa matalauta a kauyuka.(Bako)