Kuma Mr.Ban ya jaddada cewa, ba za a iya kawar da talauci ba, face sai an sa kaimi ga kasa da kasa su bi hanyar samun dauwamammen ci gaba.
A wannan rana, shugaban babban taron MDD karo na 68 John W. Ashe ya ba da wata sanarwa, inda ya yi kira ga kasa da kasa da su dukufa wajen taimakawa masu fama da talauci ta yadda za su iya shiga daftarin neman bunkasuwa da ya hada da bangarori daban daban da abin ya shafa bayan shekarar 2015. Cikin sanarwar, Mr.Ashe ya bayyana cewa, a halin yanzu, mutane sama da biliyan 1.2 ne suke fama da tsananin talauci, har kudin zaman rayuwa da kowanensu ke samu a kullum bai kai dallar Amurka 1.25 ba a kowace rana, kullum suke fama da matsalar rashin adalci da kuma bambancin da ake nuna musu.
Bugu da kari, Mr.Ashe ya nuna fatan cewa za a ci gaba da bayar da muhimmanci ga ayyukan kawar da talauci don ciyar da ayyukan bunkasuwar kasa da kasa gaba, kuma ya kamata a tabbatar sanya masu fama da talauci cikin daftarin neman bunkasuwa da ya hada da bangarorin daban daban da abin ya shafa bayan shekarar 2015. (Maryam)