in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya dandalin tattaunawa na manyan shugabanni don rage talauci da samun bunkasuwa a Beijing
2013-10-17 16:15:13 cri

Ranar 17 ga watan Oktoba na shekarar 2013, rana ce ta kawar da talauci a duniya karo na 21, a wannan rana, kasar Sin da MDD cikin hadin gwiwa sun shirya wani dandalin tattaunawa na manyan shugabanni don rage talauci da samun bunkasuwa a birnin Beijing, babban birnin kasar Sin.

A bikin bude dandalin, an karanta gaisuwa daga babban sakataren MDD Ban Ki-moon, gaisuwar murnar bude dandalin tattaunawa don rage talauci a kasar Sin, takardar ta ce, MDD tana kokari sosai don kawar da talauci a duk duniya domin cimma burin muradun karni na shekara ta 2000 na samun bunkasuwa. Ta kara da cewa, a yayin da ake samun bunkasuwa, kamata ya yi a mai da hankali kan mata, da yara, da nakasassu wadanda su kan fuskanci matsalar talauci a zaman rayukansu.

A nasa jawabi, mataimakin firaministan kasar Sin, kuma shugaban hukumar ba da taimako ga matalauta ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Mista Wang Yang ya bayyana cewa, a halin yanzu kasar Sin tana kokarin samun bunkasuwa cikin dogon lokaci, amma tana fuskantar wasu matsaloli, wadanda suka hada da rashin daidaito wajen samar da guraben aikin yi, da karuwar gibin kudin shiga da jama'ar Sin ke samu a yanzu da dai sauransu, sabo da haka, kasar Sin za ta yi iyakacin kokarin ta domin kafa wani tsari mai adalci ta yadda za a kawar da talauci a kasar Sin, kuma tana son hada kai da MDD da sauran kasashen duniya domin samar da wata duniya mai watada.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China