A wannan rana, lokacin taron kwamitin kula da harkokin tattalin arziki na babban taron MDD, Wang Min ya bayyana cewa, a matsayin babbar kasa mai tasowa, kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da harkokin kasa bisa manyan tsare-tsaren bude kofa ga waje da kuma cimma moriyar juna, kuma tana ba da taimako ga sauran kasashe masu tasowa gwargwadon karfinta bisa ka'idar hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashe masu tasowa.
Bugu da kari, Mr.Wang ya bayyana cewa, tun lokacin da aka shiga shekarar 2000, kasar Sin ta riga ta ba da taimako ga kasashe sama da 120. Gwamnatin kasar Sin tana son ci gaba da sa hannu cikin harkokin hadin gwiwar tsakanin kasa da kasa, da kuma ba da taimako ga kasashe masu tasowa don cimma burin muradun karni na MDD da ke nufin kakkabe talauci da sauri. (Maryam)