A jawabin sa wajen taron Wang Yang ya jaddada cewa, kamata ya yi a kara kokarin koyo da fahimtar tunanin kwamitin tsakiyar JKS kan kawar da talauci a sabon zamani. Sannan in ji shi hakan zai tabbatar da zurfafa tsarin yin kwaskwarima da kirkiro sabbin fasahohi, da kuma kara saurin fitar da jama'a daga talauci, a kokarin kafa zamantakewar al'umma mai jituwa a wurare masu fama da talauci.
Ban da haka, Wang ya yi nuni da cewa, a bangaren iri na shuka na zamani akwai muhimmanci kwarai da gaske, kuma babban tushe ne na ba da kariya ga ingancin abinci na kasar Sin. Don haka kamata ya yi a kara yin kwaskwarima ga tsarin yin nazari kan sha'anin iri da kara kokarin ba da kariya ga ingancin iri da kafa sansanin iri da sauransu.(Fatima)