Kuma a wannan shekarar, taken ranar kawar da talauci ta kasa da kasa shi ne, a koyi fasahohi da darussa daga halin tsananin talauci da wasu mutane ke fama da shi, don kawar da nuna bambanci ga masu fama da wannan lalura a duniya. Mr. Ban ya kuma yi kira ga jama'ar kasa da kasa da a ji muryoyin masu fama da talauci, musamman ma tsofaffi, nakasassu da dai sauransu.
Bugu da kari, manyan abubuwa guda biyu dake gaban gamayyar kasa da kasa su ne, a inganta ayyuka ta yadda za a iya cimma burin muradun karni na MDD da ke nufin kakkabe talauci, da kuma tsara daftari na aikin kawar da talauci bayan shekarar 2015.
Kasar Sin ita ce ta farko cikin kasashe masu tasowa wajen cimma burin kawar da rabin yawan mutane masu fama da talauci, don haka Sin na fatan MDD za ta ci gaba da bayar da muhimmanci ga ayyukan kawar da talauci da kuma inganta bunkasuwar kasa da kasa a matsayin manyan ayyuka, musamman ma wajen ba da taimako kan bunkasowar kasashe masu tasowa yayin da ake kokarin tsara daftarin neman damun bunkasuwa bayan shekarar 2015.
Ran 14 ga wata, yayin da yake ba da jawabi a taron kwamitin kula da harkokin tattalin arziki na babban taron MDD, mataimakin zaunannen wakilin Sin da ke MDD Wang Min ya bayyana cewa, aikin kawar da talauci ya kasance babban kalubale ga kasa da kasa, kana babban aiki ga kasashe masu tasowa muddin suna son cimma burin samun dauwamammen ci gaba, ya kamata MDD ta ci gaba da ba da taimako ga kasashe masu tasowa ta yadda za su iya karfafa ayyukansu wajen kawar da talauci. (Maryam)