in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na girmama da kuma goyon bayan hanyar da jama'ar kasar Masar suka zaba wajen raya kasar su bisa hakikanin yanayin kasar ta su
2013-12-05 16:48:40 cri

Kasar Sin na girmama da kuma goyon bayan hanyar da jama'ar kasar Masar suka zaba wajen raya kasar su bisa hakikanin yanayin kasar ta su.

Manzon musamman na kasar Sin kan batutuwan da suka shafi Gabas ta Tsakiya Mista Wu Sike ne ya bayyanawa manema labaru hakan, yayin ziyarar da ya kai birnin Alkahira a ran 4 ga wata. Mr. Wu ya kara da cewa, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakanin ta da Masar. Game da batun daidaita matsalar kasar Sham, Wu ya ce kasar Sin tana fatan za a aiwatar da matakan siyasa, tare da daidaita matsalar makamai masu guba na kasar yadda ya kamata, ta hanyar bin wadannan hanyoyi biyu a lokaci guda.

Game da sauyin yanayin siyasar kasar ta Masar a 'yan kwanakin baya, Mista Wu ya ce,

'Muna girmama, da goyon bayan hanyoyin da jama'ar kasar Masar suka zaba, bisa hakikanin yanayin kasar su, mu fadi hakan, kuma muna kan wannan manufa tamu. Don haka muka amince da cewa, duk irin binciken da jama'ar kasar Masar suka yi don neman hanyar da za su bi, Sin za ta fahimce su, ta kuma goya masu baya, muna kuma adawa da tsoma bakin wasu kasashe cikin harkokin gidan kasar ta Masar.

Wu Sike ya kara da cewa, kasar Masar tana da muhimmanci ga shiyyar da take, kuma makomarta za ta yi tasiri matuka ga ci gaban wannan shiyya. Sabo da haka ya yi fatan bangarorin da abin ya shafa za su tallafa, wajen kafuwar yanayin zaman karko a kasar ta Masar, ta hanyoyin tabbatar da tsari, da fahimtar juna, da kuma tuntubar juna. Wu ya kara da cewa, kasar Sin tana fatan kara hadin kai da kasar Masar a fannonin siyasa, tattalin arziki, da musayar al'adu da dai sauransu. Game da haka, Mr. Wu ya ce,

Duk da irin sauyin yanayin da aka samu a kasar ta Masar, da ma shiyyar baki daya, har kullum kasar ta Sin na mai da hankali sosai kan dangantakarta da Masar, sauyawar yanayi ba zai kawo wata illa ga matsayin abokantakar gargajiya da dangantakar hadin kai bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin Sin da Masar ba.'

Da ya tabo batun taron Geneva karo na biyu, kan batutuwan da suka shafi kasar Sham da za a gudanar daga ranar 22 ga watan Janairun shekara mai zuwa, Mista Wu ya bayyana cewa, daidaita matsala ta hanyar siyasa, hanya ce daya tilo da ake iya bi wajen daidaita matsalar kasar ta Sham, daga nan sai ya yi fatan za a tafiyar da yunkurin siyasa, tare da daidaita matsalar makamai masu guba, wajen daidaita matsalar kasar Sham, wato ta hanyar bin wadannan hanyoyi biyu a lokaci guda. Game da haka, ya ce,

'Daidaita matsalar Sham ta dogara ga ko za a iya bin hanyoyi biyu da na ambata ko a'a, game da aikin sarrafa makamai masu guba na Sham, ana tafiyar da wannan aiki a mataki na farko da kyau, amma a sa'i daya kuma, abin tambaya shi ne ta yaya za a amfana da fannin siyasa?, ta wace hanya za a iya jagorantar wannan amfani yayin shawarwarin da ake yi na daidaita rikicin kasar ta Sham? Wannan dai ya danganta da sakamakon taron na Geneva karo na biyu.'

Mista Wu ya yi nuni cewa, babu wani bangare da zai cimma nasara da karfin soja kan matsalar kasar ta Sham, idan har ba a daidaita wannan matsala yadda ya kamata ba, hakan zai kawo babbar illa ga dukkanin shiyyar da Sham take ciki. Sabo da haka, Mista Wu ya bayyana fatan cewa, bangarorin da abin ya shafa za su nuna dattaku, wajen shiga yunkurin daidaita matsalar kasar ta Sham ta hanyar siyasa. Ya ce,

'Ban da gwamnatin Sham da 'yan adawa, wasu manyan kasashen duniya, da kasashe masu muhimmanci a wannan shiyya suna da tasiri ga kasar ta Sham, wani abu mai muhimmanci shi ne, wadannan bangarorin da muka ambata suna mai da hankulansu kan moriyar Sham, da moriyar jama'ar ta, idan suka dada la'akari da hakan, za su samar da tallafi ga daidaita matsalar kasar ta Sham.'

Bisa labaran da muka samu, an ce, bayan da ya kammala ziyararsa a kasar Masar, Mista Wu Sike zai kuma wuce kasar Bahrain don halartar taron tattaunawa na Manama, inda zai yi musanyar ra'ayoyi da bangarorin masu ruwa da tsaki, kan yunkurin shimfida zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, da tabbatar da aikin tsaro a tekun Parisa da dai sauran batutuwa.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China