in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Masar ya yaba wa matsayin kasar Sin
2013-12-13 17:34:15 cri

Bisa gayyatar da ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya yi masa, ministan harkokin wajen kasar Masar Mista Nabil Fahmi, zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin daga ranar 14 zuwa 16 ga watan Disambar nan.

Kafin zuwansa kasar ta Sin, Mista Fahmi ya zanta da manema labaru na kasar Sin a ma'aikatar harkokin wajen Masar, inda ya yabawa kasar Sin kan matsayin ta na kin goyon bayan tsoma bakin kasashen waje cikin harkokin kasashen na kashin kan su.

Tun da fara Mista Fahmi ya ce, ana mai da hankali kwarai ga dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Masar, wanda hakan ya kusanto da dangantakarsa da manema labaru. Don gane da batun yadda ake raya dangantakar da ke tsakanin Sin da Masar a cikin sauyin yanayin siyasar kasar kuwa, Mista Fahmi ya jaddada Kalmar 'girmamawa', yana mai cewa,

'Ina so in bayyana yabo ga matsayin da Sin take dauka wajen raya dangantakar da ke tsakaninta da Masar. A mu'ammalar mu sau da yawa na fahimci cewa bisa ga ra'ayin jin kai, kasar Sin na nuna damuwarta ga sauyin yanayin siyasa a Masar, da kuma rasuwa da jikkatar da jama'a ke yi, a sa'i daya kuma, kasar Sin ta bayyana matsayinta a fili na girmama mulkin kai da martaba harkokin cikin gidan sauran kasashe, baya ga batun rashin tsoma baki cikin harkokin gidan saura kasashe. Ban da wannan, kasar Sin tana yiwa kasar Masar fatan alheri, da fatan taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa, da na shiyya shiyya kamar yadda take a da. Sabo da haka ne ma a gani na, a halin da ake ciki kasashen Sin da Masar ke ci gaba da raya dangantakarsu matuka.'

Mista Nabil Fahmi ya kara da cewa, bangarori daban daban dake Masar, sun kokarta kwarai wajen yin gyare-gyare kan daftarin tsarin mulkin kasar, kuma shugaban wucin gadi shi ma zai sanar da lokacin gudanar da kuri'ar raba gardama, kan daftarin tsarin mulkin kasa. Ya ce yana fatan kasar Masar za ta iya kaiwa ga cimma yanayin karko a fannin siyasa, a sa'i daya kuma za ta samu bunkasuwar tattalin arziki. Game da haka, ya gabatar da wasu batutuwa masu fiffiko da kasar ta Masar ta sanya gaba, Ya ce,

'Wasu masu zuba jari da na tumtuba sun gano kyakkyawar makomar Masar a fannin tattalin arziki. Ga misali Masar tana da jama'a da yawansu ya yi kusan miliyan 90, yawancinsu kuma matasa ne, ban da wannan, kasar tana da matsayi mai muhimmanci a duniyar Larabawa da nahiyar Afirka, haka kuma Masar ta yi kusa da nahioyin Asiya da Turai. Lallai wadannan misalai sun nuna kyakkyawar makomar Masar wajen zuba jari. Ko shakka babu, muna son kafa kasar Masar ta jama'a, muna fatan yin amfani da shirin 'taswira' da jama'a ke nuna goyon baya gare shi, don haka na ke gayawa abokammu daga kasashen waje cewa, kasar Masar ta kasance wurin da ake iya zuba jari cikin sauki, wuri ne kuma mai kyan gani ga 'yan yawon shakatawa.'

Mista Nabil Fahmi, wanda ya hau mukamin nasa ba da jimawa ba, ziyarar da zai kai kasar Sin, ta shaida matsayin maida hankali kan raya dangantakar Masar da kasar Sin. Daga nan sai ya yi fata kasashen biyu za su ci gaba da zurfafa hadin kai a fannonin gargajiya, da kuma inganta hadin kai a sauran fannoni. A sa'i daya kuma, ya ce, yana fata Sin da Masar za su kara yin mu'ammala a harkokin duniya, da na shiyya-shiyya. Game da haka, ya ce,

'Ina sha'awar tattaunawar da zan yi da gwamnatin Sin kan ci gaba da ake kokarin samu a duniya a yau, da ma sauran batutuwa, wadanda suka shafi fannoni da dama, tun daga kan gyaran MDD zuwa cinikayyar kasa da kasa, daga batun kafa dokoki, zuwa harkokin sarrafa karfin soja da dai sauransu. A gani na za mu tattauna wadannan batutuwa duka. A sa'i daya kuma, ina da sha'awa sosai kan gudanar da hadin gwiwar a tsakaninmu da kuma sauran bangarori daban daban, misalin hadin kai tsakanin Sin, Masar da duniyar Larabawa, ko tsakanin kasashen biyu da nahiyar Afirka.'(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China