in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci bangarorin Sudan ta Kudu da su tabbatar da tsaron rayukan al'ummar kasar
2013-12-21 17:21:55 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya ce yana fatan bangarorin kasar Sudan ta Kudu masu takaddama da juna, za su dauki matakan kare sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD da ma'aikatan hakar mai bisa bukatun kwamitin sulhu na MDD.

Mr. Liu ya bayyana hakan ne a jiya Jumma'a bayan kammalar taron da kwamitin sulhu na MDD ya gudana a asirce. An ce, taron ya mai da hankali ne ga tattauna yanayin da kasar Sudan ta Kudun ke ciki. A cewar Mr. Liu, yanzu haka, kwamitin na mai da hankali sosai ga yanayin da kasar Sudan ta Kudun ke ciki, ya kuma bayyana goyon bayansa ga MDD, da kungiyar tarayyar kasashen Afirka, da dai sauran kungiyoyin shiyya-shiyya, don gane da ci gaba da daukar matakan jan hankulin bangarori Sudan ta Kudun, ta yadda za su kai ga hawa teburin shawara da wanzar da yanayin zaman lafiya.

Bugu da kari, don gane da batun hare-haren da aka kai wa sojojin kiyaye zaman lafiya na MDDr, da kuma yankunan da ake hakar man fetur, Mr Liu ya bayyana cewa, bisa bukatun kasar Sin da sauran mambobin kwamitin sulhu na MDD, kwamitin ya ba da sanarwa, dake kunshe da yin kira ga bangarori kasar daban daban, da su rungumi matakan kiyaye tsaron sojojin kiyaye zaman lafiyar majalissar, da ma ma'aikata da kayayyakin aikin dake wannan wuri.

Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da kokari da hadin gwiwar sauran mambobin kwamitin sulhu na MDD, wajen ciyar da shirin shimfida yanayin zaman lafiya da lumana a kasar Sudan ta Kudu gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China