in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta janye rukunonin al'ummar ta daga Sudan ta Kudu
2013-12-19 16:24:10 cri
A ranar 18 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka Marie Harf ta bayyana cewa, Amurka ta riga ta debe rukunoni 3 na a'lummar ta dake kasar Sudan ta Kudu, kuma tana tattauna rikicin da ke ci gaba da tsananta a kasar tare da shugaban kasar Salva Kiir Mayardit.

Harf ta fidda wata sanarwa, dake cewa ma'aikatar tsaron Amurkan ta tura jiragen sama kirar C-130 guda 2, da wani jirgin saman musamman guda daya, don debo jami'an diplomasiyyarta dake kasar, da ma sauran jama'ar ta da jama'ar wasu kasashen duniya ma. Har ila yau, Amurka na ci gaba da kira ga jama'arta da ke Sudan ta Kudun, da su bar kasar tare da alkawarta karin jigilar jama'arta idan har akwai bukatar hakan.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China