Bayan aka shiga lokacin damina, an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a wurare daban daban na kasar Sudan ta Kudu, wanda ya haddasa ambaliyar ruwa a koguna da dama ciki har da kogin Nilu, sabo da haka ya lalata hanyoyin motici, gadoji da kuma kauyuka, kuma bala'in ya ritsa da jihohi 8 cikin dukkan jihohi 10 na kasar. Ya zuwa yanzu, 'yan kasar dubu 150 na fama da bala'in. Ganin cewa, za a ci gaba da yin ruwan sama a kwanaki masu zuwa, ana sa ran cewa, yawan mutanen da bala'in ya shafa zai kai dubu 300.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, ana fama da karancin muhimman abubuwa kamar tantuna, barguna, da kuma ruwan sha a yanki mai fama da bala'in. Kana sakamakon rashin isassun magunguna, ana samun yaduwar cututtuka a kasar. Don haka, gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta yi kira ga kasa da kasa da su agaza mata cikin gaggawa. (Zainab)