Kakakin rundunar sojojin kasar Philip Aguer ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, fadan ya barke ne da tsakar daren ranar Lahadi a tsohon barakin sojan kasar da ke Juba.
Ya ce, suna gudanar da bincike a kai, kuma da zarar sun samu karin bayanai, za su sanar da manema labarai.
Kafar yada labarai ta wurin Sudan Tribune ta bayyana cewa, fadan ya barke ne lokacin da bangare guda da galibinsu 'yan kabilar Nuer ne suka yi zaton cewa, an tura daya bangaren da galibi 'yan kabilar Dinka ne, lamarin da ya kara rura wutar tashin hankalin.
Ko da yake bayanai na cewa, al'amura sun lafa, amma akwai fargabar cewa, fadan na iya tashi, dalilin da ya sa aka tura sojoji zuwa muhimman wurare.
Rundunar sojojin kasar ta Sudan ta Kudu ta bukaci mazauna babban birnin kasar da su zauna a gidajensu har zuwa lokaci da al'amaru za su daidaita baki daya.(Ibrahim)