in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu kasashen Turai sun debe jama'ar su daga Sudan ta Kudu.
2013-12-20 11:01:56 cri
Sakamakon rikicin dake ci gaba da tsananta a kasar Sudan ta Kudu, kasashen Birtaniya, da Faransa, da Jamus sun fara aikin debe jama'ar kasahen su daga kasar.

A ranar 19 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Birtaniya ya bayyana cewa, a wannan rana, Birtaniya ta tura jirgin sama na musamman don debe al'ummar ta dake zama a kasar. Yace ya zuwa tsakar ranar ta 19 ga wata, 'yan kasar Birtaniya kimanin 150 ne suka tuntubi ma'aikatar harkokin wajen kasar, ciki har da wasu mutane da ba ma'aikatan ofishin diplomasiyya ba ne.

Har wa yau dai a wannan rana, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa Romain Nadal, ya bayyana cewa Faransa ta shawarci jama'ar kasar ta dake Sudan ta Kudun, da su fice daga wannan kasa. Kuma ofishin jakadancin kasar Faransan dake kasar Sudan ta Kudu na kokarin tuntubar Faransawa sama da 60 dake kasar, domin kara fahimtar yanayin da ake ciki.

Haka zalika a wannan rana kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Jamus da na ma'aikatar tsaron kasar sun tabbatar da cewa, 'yan kasar ta Jamus kimanin 100 ne ke zaune a yankin Juba, amma tuni ma'aikatar tsaron kasar ta tura sojojin sama don kwashe su daga wannan yanki. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China