in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su ci gaba da taimakawa Sudan ta Kudu
2013-11-19 11:11:36 cri
A ranar 18 ga wata, zaunannen wakilin kasar Sin a M.D.D. Liu Jieyi ya bayyana cewa, halin da kasar Sudan ta Kudu ke ciki ya ci gaba da tsananta, kasar Sin ta nuna goyon baya game da kokarin da gwamnatin Sudan ta Kudu ta yi, kuma ya yi kira ga M.D.D. da kasashen duniya da su ci gaba da taimakawa Sudan ta Kudu.

A wannan rana, a matsayin shugaban karba-karba na kwamitin sulhu na M.D.D. na wannan wata, Mista Liu ya shugabanci taron, inda ya saurari rahoton da manzon musamman na sakatare janar na M.D.D. ya bayar, game da ayyukan tawagar musamman ta M.D.D. a kasar Sudan ta Kudu. A cikin shawarwarin da aka yi bayan taron, kasashe mambobin kwamitin sulhu na M.D.D. sun tattauna sosai game da batun.

Bayan taron, Liu Jieyi ya fada wa kafofin yada labaru game da yadda taron yake, da kuma matsayin da kasar Sin ta dauka a kai, inda ya ce, kasar Sudan ta Kudu tana kokari wajen karfafa karfin gwamnatin da kafa tsarin kasar, kuma tattalin arzikin kasar ya samu habaka, sannan kuma yanayin tsaro da ake ciki ya samu kyautatuwa. Tawagar musamman ta M.D.D. da ke Sudan ta Kudu ta shawo kan kalubalen da ta fuskanta, ta samu gudanar da ayyukan ta yadda ya kamata, don haka kasar Sin ta yaba ma wannan sosai.

Liu ya kara da cewa, yanayin tsaro da ake ciki a kasar yana da tsanani, akwai tashe-tashen hankali tsakanin kabilu daban daban a jihar Jonglei, abin da ya sa yanzu gwamnatin Sudan ta Kudu take daukar matakai, don magance hakan, dangane da hakan, kasar Sin tana nuna goyon baya ga kokarin da gwamnatin Sudan ta Kudu take yi, kuma tana fatan gwamnatin Sudan ta Kudu da tawagar musamman ta M.D.D. da ke kasar Sudan ta Kudu za su inganta hadin gwiwa,

Daga nan sai Liu Jieyi ya yi kira ga M.D.D. da kasashen duniya da su ci gaba da taimakawa gwamnatin Sudan ta Kudu, ya bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta tura ma'aikatan wanzar da zaman lafiya kimanin 357 cikin tawagar musamman ta M.D.D. zuwa Sudan ta Kudu, sannan kuma za ta ci gaba da nuna goyon baya game da aikin tawagar a Sudan ta Kudu. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China