in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawo kan rigingimu a Afrika zai kan gaba a taron Paris
2013-12-04 10:04:47 cri

Kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samo mana labarin cewa, kasar Faransa za ta shirya wani babban taro na yini biyu daga ranar Jumma'a mai zuwa 6 ga wata, da zummar samar da hanyar da za'a inganta tsaro da kuma zaman lafiya a kasashen Afrika.

Bisa gayyatar shugaban kasar Faransa Francois Hollande, ana sa ran wakilan kasashen Afrika 42 za su halarci wannan babban taro a birnin Paris don mai da hankali a kan rikicin siyasa da tsaro wanda ya saka nahiyar a cikin wani hali na rashin tabbas.

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, shugabar kungiyar tarayyar kasashen Afrika Nkosazana Dlamini-Zuma da tawagogin kungiyar tarayyar kasashen Turai EU, asusun ba da lamuni na duniya IMF da bankin duniya su ma za su halarci taron.

A lokacin ziyararsa ta farko a nahiyar Afrika, shugaba Francois Hollande ya ce, yana kallon hanyar da za ta kawo sabuwar rayuwa mai kyau a bangaren huldar diflomasiyya tsakanin kasarsa da kasashen renon Faransa a nahiyar Afirka.

Rashin tsai da shawarar shi a game da hakan ya sa shugaban ya samu suka daga bangarori da dama, ana zargin cewa, yana son samu wani matsayi ne a fannin diflomasiyya, shi ya sa ya tura sojojin kasarsa su ba da kariya a kasar Mali. Har ila yau, yana shirin kara yawan sojojin Faransa a kasar Afrika ta Tsakiya zuwa a kalla 1,000 domin kawo karshen fadan da ake yi yanzu haka. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China