in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Faransa za ta kara yawan dakarunta a CAR
2013-11-27 10:51:42 cri

Ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian, ya bayyana cewa, kasarsa za ta kara yawan sojojinta a kasar Afirka ta Tsakiya (CAR) da a kalla 1,000, da zarar an amince da kudurin da MDD za ta gabatar game da batun a mako mai zuwa, ta yadda za a taimaka wajen maido da zaman lafiya a kasar.

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Talata, yana mai cewa, shirin tallafin sojojin kasar, zai dauki tsawon wa'adin kimanin watanni 6, ko da yake hakan ya dogara ga jadawalin da MDD za ta tsara.

A jawabin da ya gabatar a babban zauren MDD, ministan harkokin wajen kasar ta Faransa Laurent Fabius, ya ce, kasar Faransa za ta kara yawan sojojinta a kasar Afirka ta Tsakiya ne da nufin taimakawa hukumomi kasar tinkarar yanayin harkokin jin kai tare da maido da harkokin tsaro a kasar.

Bugu da kari, ministan ya ce, manufar kara yawan sojojin kasar tasa a Afirka ta Tsakiya, ita ce, farfado da shirin mika mulki da tattalin arzikin kasar da ke nahiyar Afirka. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China