A jiya Talata ne shugaban kasar Faransa Francois Hollande, ya tashi zuwa Bangui, babban birnin jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR), bayan ya halarci bikin da aka shirya a birnin Johannesburg don girmama tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu marigayi Nelson Mandela.
Shugaba Hollande ya je birnin na Bangui ne, don jinjinawa sojojin kasar Faransa guda biyu da aka kashe ranar Litinin da dare, yayin da suke aikin kwance damarar makamai daga hannun 'yan tawaye a birnin na Bangui.
Kasar Faransa dai ta tura sojoji 1,600 zuwa kasar da ta taba yiwa mulkin mallaka ne domin maido da doka da oda tare da hadin gwiwar dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar AU guda 2,500.
Bayanai daga kungiyar bayar da agaji ta Red Cross na cewa, a makon da ya gabata, daruruwan mutane ne suka halaka, a arangamar da aka yi tsakanin mayakan Seleka da magoya bayan tsohon shugaba Francois Bozize, lamarin da ake fargabar na iya haddasa wani yakin basasa, bayan kisan kiyashin da ya faru a kasar Ruwanda a shekarar 1994.
Kasar Faransa ta hanzarta tura dakaru ne bayan samun amincewa daga kwamitin sulhu na MDD, inda jami'an kasar suka yi kiyasin cewa, dakarun Faransan, za su shafe watanni 6 a aikin shiga tsakanin da suke yi karo na biyu tun watan Janairu a kasar Mali. (Ibrahim)