Majiyyar labarin ya bayyana cewa, wadannan dakarun masu dauke da makamai da ba a tabbatar da matsayinsu ba kimanin 20 sun shiga wannan wurin 'yan canji a wannan ranar ta Laraba 18 ga wata, suka kashe mutane 10 tare da kwashe makudan kudade.
A ranar 19 ga wata, wani jami'in soji na kasar Nijeriya Beyidi Martins ya fada wa kafofin yada labaru cewa, bayan da aka kai harin, sojoji sun gano wadanda suka kai harin a wani kauye da ke yankin Mubi, kuma a lokacin da suka yi musayar wuta, an kashe maharan 12, kuma an yi ganimar wasu kudade da makamai.
Tun daga shekarar 2011, ake ta fuskantar tashin hankali a wannan yankin na arewacin kasar Nijeriya, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da wadanda suka jikkata sama da 100. A watan Mayu na bana, shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya sanar da kafa dokar ta baci a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, inda aka tura sojoji da dama a wadannan wurare.(Bako)