in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin kasar Sin TEC zai gudanar da kwangilar ginin gadar sama mai tsawon KM 1.7 a jihar Kano ta arewacin Njeriya kan kudi N10 billion
2013-12-13 21:33:36 cri

Gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya ta kulla yarjejeniyar kwangilar gina gadar sama mai tsawon kilomita 1.7 kan kudi sama da naira buliyan goma da wani kamfanin kasar Sin mai suna TEC.

Kwamashinan ayyuka na jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusuf shin e ya sanya hannu a madadin gwamnatin Kano sai kuma Mr. Liu ya sanya a madadin kamfanin TEC.

Dayake jawabi kwamshinan ayyukan na jihar kano yace an bayar da kwangilar ga kamfanin kasar Sin ne sabo da nagartar aikin sad a kuma kokarin kammala aikin da ake bashi akan lokaci.

A sabo da haka ne ma ya bukaci kamfanin daya tabbatar ya kammala wannan aikin gada nan da shekara guda kacal.

Gadar kamar yadda bincike ya nuna itace gada mafi tsawo a duk fadin tarayyar najeriya, wadda ta tashi daga hanyar murtala muhammed zuwa hanyar filin jirgin sama ta bi ta kamfanin coca-cola zuwa shatale-talen `yan kura zuwa unguwar Fagge inda zata kare a kamfanin buga jaridun Triumph.

Alhaji Abba kabir Yusuf ya bukaci kamfanin daya bi ka`idojin kwangilar kuma yayi amfani da kayan aikin masu nagarta.

Kwamashinan ya ja hankalin kamfanin cewa ya sani fa akwai kamfanoni da dama da suka nemi a basu aikin, amma gwmamnati tag a ya fi dacewa ta bashi aikin, a don haka ya yi kokarin ganin bai baiwa gwmnati kunya ba.

Kwamashinan ayyukan na jihar Kano ya bayyana gamsuwar gwmnatin jihar kano game da aikin ginin wata gadar da kamfanin na TEC ke gudanarwa a halin yanzu a cikin birnin Kano wanda ake daf da karasa aikin sa.

Yayi alkawarin cewa daga yanzu har zuwa karewar wa`adin gwmanatin Kano karkashin jagorancin Injiniya Rabi`u Musa kwankwaso za a cigaba da aiki tare da kamfanin na kasar Sin.

Dayake nasa jawabin, wakilin kamfanin gine- gine na TEC Mr. Liu ya yi alkawarin gudanar da aikin mai inganci, tare da kammala shi akan lokacin da aka debar masa.

Ya yaba bisa yadda gwamnatin jihar kano ke hurda da kamfanonin kasar Sin wajen aiwatar da ayyukan raya kasa.

A halin yanzu dai kamfanin gine gine na kasar Sin TEC yana aiwatar da manyan ayyuka da dama da kudin su yah aura naira buliyan 15 a jihar kano.

Ayyukan sun hadar da gina manyan titunan mota, da filin wasan motsa jiki na zamani .(Garba Abdullahi Bagwai)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China