Zaunannen wakilin hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, kuma shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang ya gana da shugaban Jam'iyyar PDP ta kasar Nijeriya Alhaji Bamanga Tukur a ranar Laraban 27 ga wata a nan birnin Beijing.
A lokacin ganawarsu, Zhang Dejiang ya ce, JKS da PDP dukkansu jam'iyyu ne da ke kan karagar mulki, wadanda suke daukar nauyin da ke bisa wuyansu na raya kasa, sabo da haka karuwa da juna a fannin tafiyar da harkokin kasa yana da muhimmanci sosai a tsakaninsu domin ta haka ne za su iya karfafa kwarewarsu na tafiyar da ikon mulki, da sauke nauyi dake wuyansu yadda ya kamata.
Mr Zhang ya kuma lura cewa, kamata ya yi bangarorin biyu su kara mu'ammala da juna, da kara amincewarsu a fannin siyasa, da kara daga matsayin hadin kansu, a kokarin bunkasa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu.
A nashi bangaren Alhaji Bamanga Tukur ya bayyana cewa, ziyararsa a kasar Sin ta kara fahimtar juna da hadin kai a tsakanin jam'iyyun biyu, kuma ya koyi wassu darussa daga JKS, wanda ta haka zai iya inganta akidar Jam'iyyar PDP wajen tafiyar da harkokin gwamnati.(Danladi)