Majiyar 'yan sandan ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, maharan sun mamaye birnin ne tare da kaddamar da hare-hare a jere kan runduna ta 79 ta mayakan saman kasar, Batalita ta 33 ta mayakan atilari da tashar manyan motocin daukar kaya da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Kano.
Wata majiyar soja ta bayyana hare-haren da suka yi sanadiyar mutuwar wani jami'in soja a matsayin munanan hare-hare.(Ibrahim)