A ran 10 ga wata, an shirya bikin kammala aikin gyaran ayyukan more rayuwar jama'a da kamfanin CGGC na Sin da ya dauki nauyin ginawa a birnin Lagos, tarayyar Nijeriya.
Bisa abubuwan da aka tanada a cikin ayyukan, kamfanin kasar Sin ya yi gyare-gyare kan tituna 16, da hanyoyi masu tsawon kilomita 1039, da bututun fitar da ruwa a Lagos, bisa kwangilar aikin ta dalar Amurka miliyan 26 da dubu 700, bayan an fara aikin a cikin watan Maris na shekara ta 2010.
Kammala wadannan ayyuka zai kara kyautata muhallin zama da zirga-zirgar a birnin na Lagos.
Wannan biki da aka shirya a ran 10 ga wata ya samu halartar Gwamnan Lagos Baba Tunde Fashola da kuma mataimakin karamin jakadan Sin da ke Lagos Mista Qiu Jian tare da mutanen birnin na Lagos. A cikin jawabinsa, mista Fashola ya nuna godiya ga kamfanin CGGC da ya gama wannan aiki cikin lokaci kuma yadda ya kamata, tare da fatan jama'a za su yi amfani da wadannan ayyukan more rayuwar jama'a da kyau tare da ba su kariya.
CGGC kamfani ne dai da ya kware game da ayyukan samar da wutar lantarki ta karfin ruwa da gine ginen hanyoyi, kuma kamfanin ya taba gudanar da manyan ayyuka fiye da 30 a kasashen waje, sakamakon hakan kamfanin CGGC ya shahara sosai a ketare.(Danladi)