Madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta bayyana a ranar 19 ga wata a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta damu kan yadda rikici ya abku a kasar Sudan ta Kudu wanda ya yi sanadiyar rayuka da jikkatar mutane da yawa, Sin na fatan ganin bangarorin kasar da wannan riciki ya shafa za su warware matsalarsu ta hanyar shawarwari, tare da maido da kwanciyar hankali a kasar.
Bayanai na nuna cewa, rigingimu sun barke a wasu yankunan kasar Sudan ta Kudu a kwanakin da suka wuce, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa. A nasa bangaren, babban magatakardan MDD mista Ban Ki-moon ya nuna damuwa kan lamarin. (Bello Wang)