in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a warware rikicin Sudan ta Kudu ta hanyar siyasa, in ji Ban Ki-moon
2013-12-19 10:58:43 cri

Rikicin da ake fuskanta a halin yanzu a kasar Sudan ta Kudu na bukatar mafita ta hanyar shawarwarin siyasa, in ji sakatare janar na MDD, mista Ban Ki-moon a ranar Laraba tare da yin kashedi kan zafafar tashe-tashen hankali dake gudana a babban birnin kasar dake iyar bazuwa zuwa sauran yankunan kasar mafi karancin shekaru daga kafuwa a duniya. "Ina damuwa sosai da halin da kasar take ciki yanzu." in ji mista Ban a gaban 'yan jarida bayan wani zaman taron ba da bayani na kwamitin tsaro na MDD kan kalubalolin tsaro da na zaman lafiya da ake fuskanta a Afrika.

Mista Ban ya bayyana cewa, wannan rikici ne na siyasa, kuma ya kamata a warware shi ta hanyar shawarwarin siyasa. Akwai hadarin bazuwar wannan rikici zuwa sauran wasu kasashe, kuma muna da alamun dake nuna haka.

Kazamin fada tsakanin mambobin rundunar sojojin kasar Sudan ta Kudu a Juba, babban birnin kasar ya zo da wani yunkuri na juyin mulki wanda ya haddasa mutuwar daruruwan mutane, da yawancinsu fararen hula ne.

Kuma rikicin ya bazu zuwa birnin Bor mai fama da tashin hankali a ranar Laraba, lamarin da janyo damuwa ga bazuwar wani yakin basasa, a cewar wasu rahotonni.

"Na samu tattaunawa tare da shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir a ranar jiya da safe, domin bukatar shi da ya yi duk wani kokarinsa na kawo karshen wannan rikici da tabbatar da 'yancin 'dan adam da tsaro a kasar, tare da nuna masa wajabcin sake komawa teburin shawarwari tare da bangaren 'yan adawa." in ji mista Ban Ki-moon.

Mista Kiir ya ba da wata sanarwa a ranar Litinin cewa, an karya lagon wani yunkurin juyin mulki na wasu sojojin kasar magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar a daren wannan rana.

A ranar Laraba, shugaban kasar Sudan ta Kudu ya bayyana cewa, a shirye yake na fara tattaunawa tare da abokin adawarsa, a cewar wasu kafofin watsa labaru na kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China