in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi tir da harin da aka kaiwa fararen hula a Sudan ta Kudu
2013-10-22 13:20:21 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Sudan ta Kudu ko UNMISS a takaice, ta bayyana matukar bacin ranta game da mummunan harin da aka kaiwa fararen hula a jihar Jonglei a ranar Lahadin da ta gabata.

Kimanin mutane 40 ne dai suka rasa rayukansu, baya ga wasu mutane 60 da suka jikkata, sakamakon harin da aka ce wata kabila dake hamayya da al'ummar gabashin Twic sun kaddamar kan fararen hula. Dama dai wannan yanki na shan fama da fadace-fadace tsakanin al'ummunsa, wadanda su da dama, ke dauki ba dadi da juna kan batun mallakar filaye da shanun kiwo.

Da yake karin haske don gane da wannan lamari, kakakin MDD Martin Nesirky, ya ce, tuni tawagar ba da agajin jin kai ta MDD ta aika da jirgi mai saukar ungulu don dabe wadanda suka jikkata zuwa yankunan Bor da Juba. Ya ce, an kuma aika da tawagar jami'an lafiya domin gudanar da ayyukan jiyya.

Har ila yau, Nesirky ya ce, wasu jami'an tawagar sun yi sintiri a yankin don tabbatar da yawan barnar da harin ya sabbaba, tare da sanya ido ga zirga-zirgar maharan. Bugu da kari, mai magana da yawun MDD ya ce, tawagar UNMISS za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da mahukuntan kasar ta Sudan ta Kudu domin tabbatar da hukunta wadanda suka aikata wannan ta'asa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China