Mahukunta a kasar Sudan ta Kudu sun ce, sun samu nasarar dakile wani yunkuri na juyin mulki, wanda tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar ya kitsa.
Wata sanarwa daga fadar gwamnatin kasar da aka fitar ranar Litinin 16 ga watan nan, ta ce, yanzu haka ana ci gaba da bincike kan al'amarin domin tattara bayanan da suka dace. Bugu da kari, wata kafar yada labaran kasar ta rawaito shugaban kasar ta Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit na cewa, akwai sa hannun wani rukuni na sojojin kasar dake birnin Juba.
Tuni dai aka bayyana kafa dokar ta baci, da hana zirga-zirgar jama'a tun daga karfe 6 na yammaci, zuwa 6 na safiyar ko wace rana har ya zuwa wani lokaci da za a sanar a nan gaba.
Dama dai rahotannin baya bayan nan sun nuna cewa, an samu baraka tsakanin sassa biyu na jam'iyyar SPLM mai mulkin kasar, don gane da korar mataimakin shugaban kasar da shugaba Kiir ya yi cikin watan Yulin da ya gabata.
An ce, wasu daga jagororin jam'iyyar sun fice daga taron majalissar gudanarwar jam'iyyar, wanda ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata, domin nuna rashin gamsuwa da abin da suka kira rashin martaba shawarwarin da ke gudana. A hannu guda kuma wani tsagin jam'iyyar ta SPLM ya yi kira ga shugaba Kiir da ya yi murabus, kada kuma ya nuna wata sha'awa ta shiga takarar shugabancin kasar yayin babban zaben shekarar 2015 dake tafe. (Saminu)