Rahotanni daga Sudan ta Kudu na cewa, wasu gungun sojoji 'yan kabilar Nuer, wato kabilar korarren mataimakin shugaban kasar Riek Machar, sun kwace wani sansanin soji dake gundumar Bor dake jihar Jonglei.
An ce, sojojin sun samu nasarar kwace wannan sansani ne, bayan da suka fitattaki sojoji masu biyayya ga shugaba Salva Kiir daga sansanin. Harin na baya bayan nan ya haddasa mutuwar wasu manyan dakarun sojin dake sansanin na Bor.
Idan za a iya tunawa, a daren ranar Lahadin da ta gabata ne fada ya barke a birnin Juba, tsakanin tsagi biyu na dakaru masu tsaron fadar gwamnatin kasar, lamarin da shugaba Kiir ya bayyana a matsayin wani yunkuri na juyin mulkin soji, da korarren mataimakinsa Riek Machar ya jagoranci shiryawa.
Dauki ba dadin da ya auku a birnin Juba ya sabbaba rasuwar akalla mutane 26, baya ga wasu 140 da suka jikkata. Har ila yau wasu kafofin yada labarun kasar sun bayyana aukuwar karin tashe-tashen hankula a kudancin birnin Juba, lamarin da suka ce ya haddasa kisan daruruwan fararen hula, halin da kuma ya zama mafi muni da kasar ta tsinci kanta ciki tun samun 'yancin kai a shekarar 2011.
Ana dai alakanta wannan lamari da barakar da ta kunno kai cikin sassan jam'iyyar SPLM mai mulkin kasar, tun bayan korar tsohon mataimakin shugaban kasar Machar, da shugaba Kiir ya yi cikin watan Yulin da ya gabata. (Saminu)