in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardar MDD ya yi kira da a gaggauta daidaita yanayin tsaro a Sudan ta Kudu
2013-12-18 09:50:06 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya yi kira ga mahukuntan kasar Sudan ta Kudu, da su gaggauta daukar matakan daidaita yanayin tsaro a Sudan ta Kudu.

Ban, wanda ya gabatar da wannan bukata yayin tattaunawarsa da shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudun ta wayar tarho, ya nuna damuwarsa ga halin da kasar ta tsinci kan ta, sakamakon yunkurin juyin mulkin sojin da bai yi nasara ba a daren Lahadin da ta gabata.

Babban magatakardar MDDr ya kuma yi kira ga dukkanin bangarorin da lamarin ya shafa da su kai zuciya nesa, tare da kaucewa daukar matakan da suka sabawa doka, musamman duba da rade-raden yunkurin gallazawa wani sashin al'ummar kasar da ake yi. Har ila yau ya bayyana bukatar da ake da ita ga mahukuntan kasar ta hawa teburin shawara ga masu adawa domin warware takaddamar dake akwai ta hanyar da ta dace, yana mai alkawarta samar da tallafin MDD a duk lokacin da bukatar hakan ta bijiro.

A cewarsa, kimanin fararen hula 13,000 ne suka fake a wani sansanin 'yan gudun hijirar majalissar dake Juba, wanda akasarin su mata ne da kananan yara.

A wani ci gaban kuma shugabar kungiyar hadin kan Afirka uwar gida Nkosazana Dlamini-Zuma, ta yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki ga batun yunkurin juyin mulkin da ya gabata a Sudan ta Kudu, da su dauki matakan warware matsalar kasar bisa doron doka. Zuma, ta bayyana damuwarta ga halin da fararen hula ka iya tsintar kansu ciki a kasar, tana mai cewa, wajibi ne dukkan sassa su kai zuciya nesa.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai shugaba Kiir ya bayyana aukuwar yunkurin juyin mulkin soji a kasar, lamarin da ya zargi korarren mataimakinsa Riek Machar da shiryawa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China