A wani ci gaban kuma korarren mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Riek Machar, ya karyata zargin da ake masa na shirya juyin mulkin soji.
Wata kafar watsa labaru ta kasar Faransa, ta rawaito tsohon mataimakin shugaban kasar na cewa, zargin da mahukuntan Sudan ta Kudun ke masa, wani sabon yunkuri ne kawai na dakile 'yan adawa. Machar ya kara da cewa, zargin da ake masa bai wuce dabarar kau da daukacin masu hamayya da shugaba Kiir daga gwamnati, da ma jam'iyya mai mulkin kasar ba.
"Babu wani yunkurin juyin mulki. Abun da ya faru a Juba, rashin fahimta ne tsakanin dakaru masu tsaron fadar gwamnatin ya haddasa shi. Ba yunkurin juyin mulki ba ne. Ba ni da wata alaka, ko masaniya don gane da wani yunkurin juyin mulki." a kalaman Machar. (Saminu)