in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakiliyar MDD ta yi kashedi kan manyan kalubalolin dake jiran Sudan ta Kudu
2013-11-19 11:00:32 cri

Kasar Sudan ta Kudu na cigaba da fuskantar manyan kalubaloli tsakanin al'ummoni da tashe-tashen hankalin keta hakkin dan Adam, in ji babbar jami'ar MDD dake kasar Sudan ta Kudu a ranar Litinin. Wakiliyar musammun ta sakatare janar na MDD game da kasar Sudan ta Kudu, madam Hilde Johnson ta shaidawa kwamitin tsaro na MDD cewa, kasar Sudan ta Kudu na cikin tsaka mai wuya, tare da jaddada matsalar da ake cin karo da ita a wasu yankunan jihar Jonglei na cigaba da tada hankali.

A kusantowar lokacin rani, shawagin gungun dakaru masu makamai da kuma na sojojin neman 'yancin Sudan zai dada karuwa, lamarin da zai kara janyo yawaitar kai hare-hare, in ji wannan jami'a.

Jonglei, ta kasance jiha mafi girma dake gabashin Sudan ta Kudu da kuma take fama da rikice-rikicen kabilu tun lokacin da wannan kasa ta samu 'yancin kai a cikin watan Yulin shekarar 2011.

Rikicin kabilu a jihar Jonglei ya janyo asarar rayuka da dama tare da tilastawa dubun dubatar mutane barin gidajensu.

Tawagar MDD dake kasar Sudan ta Kudu ta bullo da wani jerin shirye-shirye domin fuskantar da wadannan matsaloli da kare fararen hula, in ji madam Johnson tare da bayyana cewa, jami'an tsaro a wadannan yankuna suna cin zarafin mutane da keta hakkin dan Adam, har illa yau kuma suna muzgunawa ma'aikatan MDD, jami'an diplomasiyya da sauran mutane. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China