in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sandan kasar Kongo(Brazzaville) sun cafke babban jami'in dake da hannu cikin fashewar bom a wuraren ajiye makamai na kasar
2013-12-17 17:04:29 cri
A ranar 16 ga wata, a birnin Brazzaville, 'yan sandan kasar Kongo(Brazzaville) sun yi musayar wuta da dakarun da ke goyon bayan tsohon mataimakin sakatare janar na kwamitin tsaron kasar Marcel Ntsourou, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 18, sannan 'yan sandan sun cafke Marcel Ntsourou.

A wannan rana, 'yan sanda sun yi yunkurin shiga gidan kwana na Ntsourou don gudanar da bincike, abin da ya kawo fada da dakarun da ke goyon bayan Ntsourou kimanin 100, inda aka yi musayar wuta, daga karshe Ntsourou ya mika kansa ga 'yan sanda.

An samu wanzuwar zaman lafiya da doka daga bisani a babban birnin kasar, sannan a wannan rana, 'yan sanda sun ba da sanarwar cewa, wassu dakaru masu dauke da makamai sun kai musu hari a ranar Lahadi 15 ga wata, daga bisani kuma, an gano cewa, akwai alakar tsakanin wadannan dakarun da Ntsourou.

Ana tuhumarsa ne da laifin boye makamai, da kafa dakarunsa, daga bisani kuma, an ba da sammacin bincike inda aka danka wa 'yan sanda iznin binciken gidan Ntsourou.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China