Wani babban jami'in 'yan tawayen M23 ya ce, a ranar 4 ga wata, kungiyar M23 da gwamnatin kasar Congo Kinshasa sun cimma matsaya guda game da abubuwan da za a tanada cikin yarjejeniyar samar da zaman lafiya da za su daddale, amma yayin da wakilan gwamnatin kasar suka isa birnin Kanpala hedkwatar kasar Uganda domin daddale wannan yarjejeniya, sun ba da shawarar canja yarjejeniyar zuwa wata sanarwa. '"Yan tawayen M23 sun bayyana cewa, ba za su amince da wannan ba, sabo da bangarorin biyu sun kammala yin shawarwari da shirin daddale yarjejeniya, ciki har da batun kwance damarar 'yan tawayen M23 da sauransu。
Har zuwa yanzu gwamnatin Kongo(Kinshasa) ba ta bada wani karin haske game da matakin data dauka kan wannan batu ba.(Bako)




