Bisa labarin da kafofin yada labaru na kasar Kogo(Kinshasa) suka bayar, an ce, a wannan rana, wannan jami'in liken asiri da ba ya son fayyace sunansa, ya bayyana a birnin Goma da ke yankin gabashin kasar cewa, yanzu, Makenga ya buya a birnin Kampala, babban birnin kasar Uganda. Yana mai cewa, sojojin kasar Uganda sun ba da tabbaci game da tsaronsa. Amma, bisa yin la'akari da batun tsaro, ba ya fayyace inda yake zama ba.
A matsayin shugaban dakarun M23, a karshen shekarar bara, M.D.D. da Amurka sun sanya sunansa cikin takardar yin takukumi, kuma yanzu, gwamnatin Kongo(Kinshasa) tana kokarin neman shi.(Bako)