A cikin 'yan makwanni kadan da suka wuce, a karkashin taimako daga tawagar samar da zaman lafiya ta M.D.D. ta MONUSCO, sojojin gwamnatin kasar sun yi ta kai farmaki ga muhimman wuraren da dakarun M23 ke mamaye a lardin North Kivu da ke yankin gabashin kasar, inda suka kwace garurruwa da dama, kuma dakarun M23 suka tsere zuwa kan tsaunuka. Ya zuwa ranar 3 ga wata da tsakar rana, bangarorin biyu sun yi ta musayar wuta, abin da Manazarta suka bayyana cewa, bayan kai farmaki ga dakarun da ke adawa da gwamnatin, akwai yiwuwa sosai bangarorin biyu za su yi shawarwari don warware rikici a tsakaninsu.
A watan Afrilu na bara, ne dai dakarun M23 suka ta da zaune tsaye a yankin gabashin kasar Kongo(Kinshasa), kuma abin da ya yi sanadiyyar jama'a dubban darurruwa sun bar gidajensu, tare da mutuwar wasu ma'aikatan kiyayen zaman lafiya na M.D.D.
A watan Disamba na bara kuma, a karkashin shiga tsakani daga bangarorin da dama, gwamnatin Kongo(Kinshasa) da dakarun M23 sun yi shawarwari a birnin Kampala hedkwatar kasar Uganda, amma, an kasa yin shawarwari a tsakaninsu.(Bako)




