in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu barkewar zazzabin cizon sauro a kasar Kongo(Kinshasa)
2013-11-22 16:58:50 cri

Kungiyar likitocin nan ta na gari na kowa wato 'Doctors Without Borders' ta bayar da wata sanarwa a ran 21 ga wata cewa, an samu barkewar cutar zazzabin cizon sauro a yankin Rutshuru na jihar Nord-Kivu da ke gabashin kasar Kongo(Kinshasa) a 'yan kwanakin baya, inda jama'a fiye da dubu 24 suka kamu da wannan cuta a cikin watanni hudu da suka gabata.

Kungiyar ta shaida wa manema labaru a wannan rana cewa, daga farkon watan Oktoba zuwa yanzu, yawan mutanen da suke kamu wa da cutar a ko wane mako a yankin Rutshuru ya kai kusa dubu 3, wanda ya ninka sau 2.5 bisa ga layin gargadi da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta tsara kan cututtuka masu yaduwa.

A cewar kungiyar, ban da salon yaduwar cutar, karancin kayayyakin a fannin kiwon lafiya a kasar Kongo(Kinshasa) sun sanya jama'a da dama ba su samun kulawar lafiyar da ta kamata.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China