in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasar Kongo(Brazzaville) za ta kasance mai ma'anar tarihi
2013-03-28 15:15:52 cri
A ranar 27 ga wata, a birnin Durban da ke kasar Afrika ta Kudu, yayin da shugaban kasar Kongo(Brazzaville) Denis Sassou Nguesso ke zantawa da manema labaru, ya bayyana cewa, yana sa ran ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasarsa, kuma yana gani cewa ziyarar za ta zamo mai ma'anar tarihi.

Sassou ya bayyana cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Kongo(Brazzaville) da Sin na da dadadden tarihi, kuma a shekara mai zuwa, za a yi bikin cika shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya da ke tsakaninsu. Shugaba Xi zai zama shugaban kasar Sin na farko, da ya yi tattaki zuwa kasar, kuma yana fatan wannan ziyara za ta ci gaba da karfafa dangantakar kasashen biyu. Haka kuma, shugaba Nguesso zai yi amfani da wannan dama don yi shawarwari da Shugaba Xi game da batun hadin gwiwar tattalin arziki, da sauran batutuwan duniya da suka dora muhimmanci sosai a kai, tare da batun samar da zaman lafiya da tsaro a kasashen Afrika,

A wannan rana, Nguesso da sauran shugabannin kasashen Afrika sama da 10, sun halarci shawarwarin da ke tsakanin shugabannin kasashen Afrika da na kasashen BRICS. Yayin da yake zantawa da manema labaru game da batun kafa bankin raya kasashen BRICS, shugaban ya ce, nan gaba, wannan banki zai kara alfanun da ake samu daga bankin duniya, da bankin raya kasashen Afrika, kuma kasashen Afrika za su yi farin ciki da hakan.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China