A cikin sanarwar, Robinson ta bukaci gwamnatin Kongo(kinshasa) da dakarun adawa na M23, da su yi shawarwari cikin tsanaki, don warware matsalolin da ke tsakaninsu, da ingiza farfado da halin da ake ciki a yankunan gabashin kasar. Ta jaddada cewa, cimma burin samar da zaman lafiya da karko ta hanyar siyasa, na da ma'anar musamman game da jama'ar kasar Kongo(kinshasa).
A watan Afrilu na shekarar 2012, dakarun kungiyar NCDP ta kasar Kongo(kinshasa) ta ta da bore, inda suka kafa dakarun adawa da gwamnatin kasar mai suna M23, kuma a watan Nuwambar bara, sun mamaye birnin Goma da ke lardin Nord-Kivu a yankin gabashin kasar. A ranar 7 ga watan Disamba na bara, gwamnatin Kongo(kinshasa) da dakarun M23, sun fara yin shawarwari a birnin Kampala, amma har yanzu, kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.(Bako)




