A ranar 25 ga watan Afrilu na bana ne, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri, inda aka kafa tawagar hadin gwiwa ta kiyaye zaman lafiya a kasar Mali. Bisa bukatun MDD, kasar Sin ta tsaida kudurin tura tawagar sojojin kiyaye zaman lafiya dake kunshe da sojoji masu aikin gine-gine, kiwon lafiya da kuma kiyaye tsaro guda 395 zuwa wuraren da za su yi aiki. Wannan ne karo na farko da kasar Sin ta tura sojojin tsaro da za su shiga aikin kiyaye zaman lafiya na MDD. (Zainab)