in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta zama wata babbar kasa a fannin karuwar yawan neman ikon mallakar kariyar fasahar ilmi a duk duniya
2013-12-16 17:09:06 cri

Kungiyar kare ikon mallakar kariyar ilmi ta duniya ta bayar da wani rahoto, dake kunshe da bayani kan ikon mallakar kariyar ilmi da ake neman rajistarsa a shekara ta 2013.

Rahoton wanda aka fitar a ranar 9 ga wata a birnin Geneva, ya nuna cewa a shekara ta 2012 yawan ikon mallakar kariyar ilmi da aka nemi rajista ya ci gaba da karuwa, har ya kai miliyan biyu da dubu dari uku da hamsin, hakan ya sa shekara ta 2012 ta zama shekara da aka fi samun saurin karuwarsa a cikin shekaru goma sha takwas da suka gabata, wani muhimmin dalilin da ya sanya haka shi ne, saurin karuwar ikon mallakar kariyar ilmi da aka nemi rajista a kasar Sin.

Wannan rahoto na shekarar 2013, rahoto ne da kungiyar kare ikon mallakar kariyar ilmi ta duniya ke bayarwa a ko wace shekara, don kidaya, da nazari kan ikon mallakar ilmi da aka nemi rajista a shekarar da ta gabata. Ikon mallakar kariyar ilmin da aka nemi rajista da aka ambata a nan ya hada da fannoni hudu, wato neman rajistar ikon mallakar kariya ilmin kirkira, da neman rajistar kananan kayayyaki, da neman rajistar alamun kaya, da kuma neman rajistar siffar kayayyakin masana'antu.

Rahoton ya nuna cewa, yawan ikon mallakar kariyar ilmi da aka nemi rajista a shekara ta 2012 a duk duniya ya kai miliyan biyu da dubu dari uku da hamsin, wanda ya fi samun saurin karuwa a cikin shekaru 18 da suka gabata. Babban darektan kungiyar kare ikon mallakar kariyar ilmi ta duniya Mista Francis Gurry ya bayyana cewa, ko da yake ana fuskantar wasu kalubaloli wajen farfado da tattalin arzikin duniya, amma yawan ikon mallakar kariyar ilmin da aka nemi rajista ya karu cikin sauri bisa ga na lokacin da aka samu rikicin tattalin arziki a shekara ta 2009. Game da haka, ya ce,

'A shekara ta 2012, yawan ikon mallakar kariyar ilmin kirkirawa ya karu da kashi tara da digo biyu cikin dari bisa ga shekarar da ta wuce, yawan ikon mallakar kariyar ilmi da aka nemi rajistar siffar kayayyakin masana'antu kuwa, ya karu da kashi goma sha bakwai bisa dari, sai yawan ilkon mallakar kariyar ilimi da aka nemi rajistar kananan kayayyaki da ya karu da kashi ashirin da uku da digo hudu bisa dari, yayin da yawan ikon mallakar kariyar ilmi da aka nemi rajistar alamun kaya ya karu da kashi shida bisa dari, dukkansu sun fi yawan karuwa bisa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, kuma sun wuce karuwar tattalin arziki na yawancin gamayyar tattalin arziki.

Rahoton ya ce, a shekara ta 2012, a cikin daukacin hukumomi biyar a fannin ikon mallakar kariyar ilmi a duk duniya, kasar Sin ta zama daya tilo da ta samu saurin karuwa fiye da kashi goma bisa dari a dukkan fannoni hudun can. Daga cikinsu kuma, yawan ikon mallakar kariyar ilmin kirkirawa ya karu da kashi ashirin da hudu, yawan ikon mallakar kariyar ilmin kirkira da mazaunan Sin suka nemi rajista ya kai dubu dari biyar da sittin, wanda ya kai matsayi na farko a duk duniya. A fannin ikon mallakar kariyar ilmi da aka nemi rajistar alamun kaya kuma, kasar Sin ta samu adadin da yawansu ya kai miliyan guda da dubu dari biyar da tamanin, wanda ya kai matsayi na farko a duniya, sai Amurka wadda ke da yawan kusan dubu dari shida, Jamus ta na da kusan dubu dari uku da casa'in. A fannin ikon mallakar kariyar ilmi da aka nemi rajistar siffar kayayyakin masana'antu kuma, kasar Sin ta gabatar da yawan da ya kai dubu dari shida da hamsin, bayanta sai kasar Jamus, wadda ta gabatar da yawan da ya kai dubu sabanin da shida. A fannin ikon mallakar kariyar ilmi da aka nemi rajistar kananan kayayyaki kuma, Sin ta gabatar da yawan da ya kai dubu dari takwas da ashirin da bakwai, wanda ya kai kashi tamanin da tara da digo biyar bisa ga dukkanin ikon mallakar ilmin da aka nemi rajista a duniya.

Babban darekta Francis Gurry ya ce, saurin karuwar yawan ikon mallakar kariyar ilmin da kasar Sin ta nemi rajista ya zama wani babban ginshiki da ya sa kaimi ga bunkasuwar ikon mallakar kariyar ilmi da aka nemi rajista a duk duniya. Game da haka, ya ce,

'Alama ta biyu da nake son fada ita ce, kasar Sin ta kara taka muhimmiyar rawa a fannin ikon mallakar kariyar ilmi a duk duniya, kamar yadda na fada sau da yawa a shekarar da ta gabata. In mun duba, muna iya ganin cewa, a dukkan fannoni hudu da muka ambata, kasar Sin ta zama daya tilo a duk duniya, wadda matsayinta ke kasancewa a gabanni biyar, kuma wadda ta samu saurin karuwa fiye da kashi goma cikin dari a ko wane fanni.'

Rahoton ya kara da cewa, hukumar lura da neman rajistar ikon mallakar kariyar ilmin kirkira ta Turai da Jamus da Britaniya sun samu karuwar yawan ikon mallakar kariyar ilmi da aka nemi rajista, amma Faransa da Italiya sun samu koma baya. A sa'i daya kuma kasashe masu tasowa sun kara dagawa a matsayinsu na duk duniya, wajen neman rajistar ikon mallakar kariyar ilmi.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China