131029murtala1
|
Taron da ya samu halartar manyan shugabanni, jami'ai da masana a fagen ilimi na Najeriya, an yi shi ne a babban dakin taro na hukumar kula da jami'o'i ta kasa wato NUC dake birnin Abuja. Ministan ilimi na Najeriya cif Ezenwo Nyesom Wike, da shugaban hukumar NUC Dr. Ahmadu Ali, da Alhaji Aminu Suleiman wanda shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin ilimi na majalisar dokokin Najeriya da dai sauran wasu manyan jami'ai ne suka halarci taron.
Daga cikin sassan ilimin da aka kaddamar a wannan karo, akwai majalisar hukumar jami'o'in kasa dake Abuja, da hukumar kula da ilimin kimiyya da fasaha dake jihar Kaduna, da majalisar kula da rajistar malaman koyarwa ta Najeriya dake Abuja, da kauyen koyon harshen Faransanci dake jihar Lagos, wato Nigeria French Language Village a turance, da kuma cibiyar koyon harsunan Najeriya dake jihar Abia. Sauran hukumomin ilimin da aka kaddamar sun hada da makarantu na musamman dake jihohin Niger, Kebbi, Taraba, Jigawa, Anambra, Bayelsa da Zamfara da sauransu.