in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara aiki da wani shirin hadin gwiwar masana ilmi tsakanin Sin da Afirka
2013-10-21 18:06:54 cri

A ranar Litinin 21 ga wata ne, aka fara aiki da wani shirin hadin gwiwa da ya shafi mashahuran cibiyoyin nazari da kuma jami'o'i a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, a kokarin kara inganta mu'amala da hadin gwiwa ta fuskar ilmi a tsakanin bangarorin biyu. Wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Mr.Yang Jiechi ya bayyana a gun bikin fara aiki da shirin cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ba kawai ta shafi harkar zuba jari ba ne kawai, a'a, har ma ya shafi musayar ilmi. Ya yi fatan masanan bangarorin biyu za su bayar da gudummawarsu ga ci gaban huldar da ke tsakanin bangarorin biyu, har ila yau, za su bayyana wa duniya ainihin gaskiyar huldar da ke tsakanin Sin da Afirka.

A shekarar 2009, gwamnatin kasar Sin ta sanar da matakai guda takwas da za a dauka da suka shafi hadin gwiwar da ke tsakaninta da Afirka, kuma yalwata hadin gwiwar da ke tsakanin masana na sassan biyu na daya daga cikinsu. A cikin shekaru hudu da suka wuce, Sin da Afirka sun gudanar da shirye-shirye sama da 100 da suka shafi nazari da harkokin dab'i, kuma an fara aiki da wannan shiri na hadin gwiwar masana ne a ranar 21 ga wata da nufin samar da wani tsari na yin musayar ilmi tsakanin Sin da Afirka. Mr.Lu Shaye, babban sakataren kwamitin bin diddigin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ya bayyana cewa, "Muna fatan shirin zai samar da wani sabon dandali na yin musayar ilmi tsakanin masanan bangarorin biyu, don inganta huldar hadin gwiwa tsakaninsu da ma masanan sauran sassan duniya, ta yadda masanan za su ba da gudummawa a kokarin da ake na kara daukaka huldar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, tare da jawo hankalin kasashen duniya kan aikin samar da zaman lafiya da ci gaba a Afirka."

Shirin ya samu karbuwa sosai daga sassan nazari na Sin da Afirka, wadanda suka nuna himmarsu ta ganin cewa an ba su dama, kuma daga karshe, an zabi sassa guda takwas daga kowane bangare a matsayin rukuni na farko na sassan nazari da za su hada gwiwa da juna, ciki har da cibiyar nazarin kimiyyar zaman takewar al'umma ta kasar Sin da hukumar nazarin harkokin zaman al'umma da kimiyya ta Afirka da jami'ar Peking da sauransu.

Wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Mr.Yang Jiechi ya halarci bikin fara shirin, inda a madadin gwamnatin kasar Sin ya taya bangarorin biyu murnar fara aiki da shirin, kuma ya bayyana fatan cewa, "kamata ya yi masana na Sin da Afirka su yi la'akari da halin da ake ciki a zamanin yanzu, su yi nazari kan kwarewar da Sin da Afirka kowanensu ke da shi a bangaren wayinkansu, don binciko hanyar samun moriyar juna a hadin gwiwar da ke tsakanin sassan biyu, sa'an nan, su ba da shawarwari ga yadda za a bunkasa hadin gwiwar sassan biyu ta fannonin tattalin arziki da ciniki da kimiyya da al'adu da kuma ba da ilmi, tare da kawar da abubuwan da ke kawo cikas ga hadin gwiwar sassan biyu da kuma bayyana wa duniya gaskiyar huldar da ke tsakanin sassan biyu."

A jawabinsa, Mr.Yang Jiechi ya kuma yi nuni da cewa, akwai kasashen da suke gaba a wajen nazarin huldar da ke tsakanin Sin da Afirka, amma ya kamata Sin da Afirka su tsaya kan matsayinsu na kansu a wannan nazarin da suke yi, don fito da muryar Sin da ta Afirka a wannan bangare.

Cibiyar nazarin harkokin duniya ta kasar Afirka ta kudu da kuma cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta kasar Sin na daga cikin abokan hadin gwiwa na farko da shirin ya zaba. Madam Elizabeth Sidiropoulos, shugabar cibiyar nazarin harkokin duniya ta kasar Afirka ta kudu ta ce, shirin zai sa babban kaimin hadin gwiwar masanan bangarorin biyu, ta ce, "A matsayina na 'yar Afirka kuma mai yin nazari, na gane cewa, huldar da ke tsakanin Sin da Afirka da kuma musayar ilmi tsakanin sassan biyu za ta iya inganta karfinmu, ta yadda mu da kanmu za mu zabi makomarmu. Mun kuma san cewa, ya kamata mu yi aiki tsakaninmu da Allah, don ba da gudummawarmu ga mahukuntan kasashen Afirka da al'ummarsu, muna bukatar kara fahimtar kasar Sin, ciki har da manufofin diplomasiyya na kasar."(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China