Bisa wata sanarwar da fadar shugaban kasar Faransa ta bayar, an ce, Francois Hollande ya bukaci ministan harkokin wajen kasar Laurent Fabius da ya je Nijeriya, domin koma da shi gida.
Shugaban Hollande ya kuma bayyana cewa, Faransa ba za ta manta da Faransawa guda 7 da ake cigaba da yin garkuwa da su a kasashen Siriya, Mali da Nijeriya, kuma Faransa za ta ci gaba da kokari, don ganin an sako su.
Bisa labarin da kafofin yada labarun Faransa suka bayar, an ce, kwanan baya, sojojin Nijeriya sun kai samame a wani girin da 'yan kungiyar Boko Haram suke tsare da Francis Collomp, mista Collomp ya samu tsira daga inda ake garkuwa da shi a yayin da bangarorin biyu suke musayar wuta.(Bako)