Kwararru daga kasashe mambobi na kungiyar ruwan teku na kasashen Afrika na yammaci da na tsakiya (OMAOC) sun yi taro a ranar Talata da ta gabata a kasar Congo domin kafa wani daftarin doka da zai taimaka wajen yaki sosai da matsalar 'yan fashin teku, da ma wasu ayyukan da ba bisa doka a kan ruwan tekun wannan shiyya.
Ministan kasar Congo kan harkokin teku, Martin Parfait Aime Coussoud Mavoungou ya yi jawabi a yayin bude taron kan muhimmancin wannan aiki dake gaban kwararrun wannan shiyya.
'Aikin dake gabanku daga bakin wannan rana ya dauki muhimmiyar hanya da kuma niyya bisa fatan gamayyar kasashen dake raba ruwan teku tun daga Mauritaniya zuwa Angola, na binciken hanyoyin da matakan da za su iyar taimaka, ta yadda kasuwanci ta hanyar ruwan teku zai kasance mai kafi a cikin wannan shiyya, bisa amincewa da wasu dokokin teku da aka tsara da gudanar da ayyukan hadin gwiwa da suka shafi kulawa taragogin kayayyaki da jiragen ruwa dake ratsa tashoshin ruwanmu, bisa tsarin dokar teku na hadin gwiwa a wannan shiyya.' in ji mista Mavoungou.
Taron Congo ya gudana bayan taron shugabannin da gwamnatoci kan tsaro da kiyaye mashigin ruwan tekun Guinea, da aka gudanar daga ranar 24 zuwa 25 ga watan Yunin da ya gabata a birnin Yaounde na kasar Kamaru. (Maman Ada)