in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da goyon bayan yaki da 'yan fashin teku a Somaliya
2013-11-19 10:23:43 cri

Wakilin din din din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya bayyana aniyar kasarsa, ta ci gaba da goyon bayan duk wani yunkuri, na dakile fashin teku a Somaliya.

Liu Jieyi, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin tsaron na karba karba na wannan wata, ya ce, kasar Sin a shirye take, da ta yi hadin gwiwa da dukkanin kasashen duniya wajen yaki da wannan mummunan laifi na fashin teku.

Wakilin kasar ta Sin wanda ya bayyana hakan jim kadan da kammala taron tattaunawar da kwamitin na tsaro ya gudanar a ranar Litinin kan wannan batu, ya kara da cewa, a baya ma kasar Sin ta tura jiragen yaki na ruwa 45, karkashin tawaga 15, wadanda ke aikin ba da kariya ga jiragen ruwa na dakon kaya kimanin 5,200 a sassan tekun kasar ta Somaliya daban daban. Ya ce, Sin na da burin ci gaba da ba da wannan gudummawa har sai kwalliya ta biya kudin sabulu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China