Kwamitin tsaro na MDD ya bayyana damuwarsa kan barazanar matsalar fashin teku a yankin ruwan tekun Guinee tare da jaddada bukatar bullo da matakan fuskantar tushen wadannan matsaloli dake janyo wannan annoba, tare da kafa dangantaka da kungiyoyin wannan shiyya tare da taimakon gamayyar kasa da kasa.
Kwamitin tsaro na nuna damuwarsa sosai game da barazanar ayyukan fashin teku da sace-sace da mamakai dake faruwa a cikin ruwan tekun Guinee wadanda suke janyo mummunan tasiri ga sufurin ruwan tekun kasa da kasa, tsaro da cigaban tattalin arzikin kasashen Afrika dake wannan shiyya, ta yadda za'a iyar tabbatar da tsaro ga mutanen dake rayuwa a yankunan ruwan teku, da ma sauran mutane, da kuma kiyaye hanyoyin jiragen ruwa na kasuwancin kasa da kasa, in ji babban taron kwamitin tsaro na MDD da wannan karo kasar Argentina take jagoranta, a cikin wata sanarwa da ake tura wa manema labarai.
Kwamitin tsaro ya nuna yabo kan dabarun da ake dauka cikin hadin gwiwa tsakanin kungiyar tarayyar Afrika, kasashen wannan shiyya da kungiyoyin shiyya-shiyya, wadanda suka hada kungiyoyin CEEAC, ECOWAS, CGG da kuma kungiyar OMAOC domin kara karfafa tsaro a yankin ruwan tekun Guinee, musammun ma a lokacin babban taron shugabanni da gwamnatocin na yankin ruwan tekun Guinee a birnin Yaounde na kasar Kamrau a ranakun 24 da 25 ga watan Julin shekarar 2013.
Hakazalika, kwamitin tsaro ya yi jinjina ta musammun kan matakin kafa wata cibiyar kula da ayyukan kasa da kasa a kasar Kamaru da za ta daukar nauyin daidaita aiwatar da dabarun kasa da kasa da na shiyya-shiyya da za su shafi illahirin yankin ruwan tekun Guinee, in ji kwamitin sulhu na MDD. (Maman Ada)