in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata gwamnatoci su kare fararen hula yayin rikici, in ji wakilin Sin
2013-08-20 14:33:13 cri

Ran 19 ga wata, a hedkwatar MDD da ke birnin New York, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD Wang Min ya jadadda cewa, ya kamata gwamnatocin kasa da kasa su dauki nauyin kare lafiyar fararen hula yayin faruwar rikice-rikice, tare kuma da mai da hankali sosai wajen yin amfani da dokokin kasa.

A wannan rana, an yi muhawara a fili kan batun game da yadda ake kare fararen hula da ke fama da rikice-rikice a yayin taron kwamitin sulhu na MDD, inda Wang Min ya jadadda cewa, fararen hula sun fi shan wahalhalun da rikice-rikice ke kawo musu, shi ya sa, ya kamata duk bangarorin da suka shiga cikin ricike-rikice su kare fararen hula bisa dokokin jin kai na duniya da dai sauran kudurorin kwamitin sulhu na MDD da abin ya shafa.

Wang Min ya nuna cewa, ya kamata a gudanar da ayyukan ba da agajin jin kai ga fararen hula bisa ka'idojin jin kai da kuma adalci, da kuma girmama ikon kasar da abin ya shafa.

Ya kuma kara da cewa, abin da ya fi muhimmanci wajen karfafa ayyukan kiyaye tsaron fararen hula shi ne yin rigakafi da kuma warware rikice-rikicen da ake fama da su. Ya kamata kwamitin sulhu na MDD ya yi kira ga kasashen da abin ya shafa da su daidaita sabane-sabane tsakaninsu a siyasance ta hanyar yin shawarwari da dai sauran hanyoyin zaman lafiya, ta yadda za a iya rage ko kawar da mutuwa ko raunutar fararen hula. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China