130718Mandela-Bako
|
Yau ranar haihuwar Nelson Rolihlahla Mandela ce wanda shekarunsa ya kai 95 a duniya, kwanan baya, halin da yake ciki ya jawo hankalin jama'ar kasashen duniya. Me ya sa wannan tsohon shugaban kasar ya jawo hankalin jama'a kamar haka, musamman ma bayan da ya sauka daga mukaminsa har na tsawon shekaru sama da 10. Yayin da mataimakin shugaban kwamitin nazarin batun Afrika, kuma mataimakin shugaban cibiyar nazarin tarihin Afrika Liu Hongwu ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa, Mista Mandela ya kawo arziki da alheri ga kasashen duniya.
Yayin da Shehun malami Liu Hongwu ke zantawa da wakilinmu, ya ce, "Kullum Shugaba Mandela ya kan ba da shawarwari na samun sulhuntawa tsakanin kabilu daban daban da zaman jituwa a tsakaninsu, wanda suka yi daidai da tunanin gargajiya na kasashen Afrika. Haka kuma, wannan tunani ya sha bamban da irin tunani na kasashen yammacin duniya wato na neman samun ci gaba ta hanyar yin hamayya, wannan tunani ya yi kira da a samu bunkasuwa cikin jituwa, da jaddada muhimmancin zaman jituwa a iyali ko zamantakewar al'umma tare."
Shehun malami Liu Hongwu yana ganin cewa, a shekarun baya, Mandela ya taba gwada daukar matakan soji don yaki da tsarin nuna bambancin launin fata, amma a karshe dai, ya canja ra'ayinsa. Har kuma, sabo da yaki da wannan tsari, aka taba tsare shi gidan yari, amma duk da haka, ya ci gaba da nuna cewa, ya kamata a kafa wani sabon tsarin zamantakewar al'umma wanda bakaken fata da fararen fata za su zama cikin jituwa. Muddin dai aka cimma wannan buri, kasar Afrika ta Kudu za ta samu makoma mai haske. A karkashin irin wannan ra'ayi, Mandale ya hambarar da tsarin nuna bambancin launin fata, kuma ya kafa sabuwar kasar Afrika ta Kudu, hanyar da ta zama alkibla ga shugabannin da suka kama mulki bayan shi, suna ci gaba da shugabancin kasar a karkashin ra'ayinsa.
Malam Liu ya kara da cewa, Mandela yana fafutukar neman zaman adalci da samun 'yanci a duk rayuwarsa. Ya jaddada cewa, kamata ya yi dukkan kasashe, da dukkan kabilu na duniya su cimma burin samun zaman adalci da 'yanci. Yana mai cewa, "Wannan 'yanci da zaman adalci ba su yi daidai da irin ra'ayin da kasashen yammacin duniya suka gabatar ba. Wani lokaci, kasashen yammacin duniya suka ce, samar da adalci da 'yanci a tsakanin kasashensu ne kawai, amma yayin da suka yi zama tare da sauran kabilu ko kasashe, sun nuna karfin tuwo gare su. Amma, ra'ayin da Mandela ya bayar, ya hada duk kabilu da mutanen kasashen duniya wuri guda."
Shehun malami Liu Hongwu ya bayyana cewa, game da batun kasa da kasa, irin ra'ayi na rashin tsoron kome da Mandela yake nunawa, da kuma tunaninsa sun karfafa zukatan kasashen da ba su da wadata sosai. Ya bayyana karara har sau da dama don yin kushewa ga kasar Amurka da ta tabka yakin Afghnistan da na Iraqi, kuma a ganin Mandela cewa, kamata ya yi kasashen yammacin duniya su dauki alhakin rikicin yankin Gabas ta tsakiya da rikicin da ke tsakanin Falesdinu da Isra'ila.
Ban da wannan kuma, Mandela ya kawo arziki da alheri ga raya zamantakewar al'umma da siyasa na nahiyar. A cikin shekaru sama da 10 da suka gabata, kasashen Afrika sun inganta shawarwari tsakaninsu, kuma an gaggauta yunkurin dunkulewar kasashen Afrika baki daya. Rikicin da ke nahiyar musamman a yankunan kudancin kasashen Afrika ya ragu sosai, wannan na da alaka sosai da irin rawar a-zo-a-gani da Mandela ya taka, Mr. Liu ya ce,"Mandela ya taka rawar shugabanci na a zo a gani wajen sa kaimi ga inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen Afrika. Ya yi ta hobbasa wajen raya zamantakewar al'umma a kasashen Afrika, sabo da a ganinsa, ya zama dole nahiyar Afrika ta inganta hadin gwiwa tsakaninsu, don kara fada-a-ji a zamantakewar al'umma."
Haka kuma, Shehun malami Liu ya ce, ra'ayin Mandela yana da ma'anar musamman kasashen duniya don su warware matsalolin da ake fuskanta a yanzu.(Bako)