Har ila yau a wannan rana babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya bayar da wata sanarwa, inda ya bayyana bakin cikinsa game da rasuwar Mandela. A cikin sanarwar, Ban Ki Moon ya yabi rayuwar Mandela, yana mai cewa, Mandela ya zama wani muhimmin gwarzo a wannan duniya, wanda ke cike da rayuwar adalci.