A cikin sanarwar ya sanar da cewa :wanan matsala za ta shafi yaran kasashe 8 na yankin sahel sabili da karamcin abinci da rashin ruwan sama ya haddasa.
Darekatan asusun yara na MDD ,ya furta cewa :duk wani gibi ta bangaren yawa ko kuma inganci na abinci a cikin gida yana zama babbar matsala ga yara da matasa..
Tun can da farko,yara da dama a yankin sahel na fuskantar matsalar cutar tamowa,wanda kuma ke kara yin kamari. A yanzu haka a dukkan sassan yankin da lamarin tamowa ya wuce intaha.
Ya jadada cewa abincin da aka sarrafa musamman domin yin amfani da shi kai tsaye,shi ne magani mafi inganci, a kokarin warkar da kananan yara yan kasa da shekaru 5 daga cutar tamowa mai tsanani.Abun da zai basu sukunin murmurewa su kuma rayu.Babbar matsalar ita ce samarwa yaran irin wannan abinci wanda zai wadatar da su. An ce bukatar irin wannan abinci za ta karuwa a nan gaba. (Abdou Halilou)