Shugaban bankin raya kasa ta Rwanda Alex Kanyankole ya bayyana cewa, rancen kudin da kungiyar ta baiwa bankin zai ba da taimako ga kasar Rwanda wajen biyan bukatun iyalan da ba su da isassun kudin shiga don sayan gidajen zama, da kuma ba da taimako a fannin samar da karin kudade wajen gina gidajen zama masu araha, sakamakon hakan, dukkan al'ummomin kasar Rwanda za su iya samu gidajen zama a karshe.
Bugu da kari, bisa hasashen da bankin raya kasa ta Rwanda ya yi, an ce, rancen kudi na dallar Amurka miliyan 10 da kungiyar gidajen zama ta nahiyar Afirka za ta baiwa bankin, a kalla zai ba da taimako ga iyalai kimanin dubu daya wajen saya a karon farko gidajen zama nasu. (Maryam)